Da yake jawabi a wani babban taron MDD domin tunawa da ranar kawar da makaman nukiliya na kasa da kasa, wanda aka saba gudanarwa a ranar 26 ga watan Satumba na kowace shekara, mista Guterres ya bayyana cewa, duniya za ta zauna lafiya ne kadai idan ya kasance ta kauracewa amfani da makaman nukiliya baki daya a doron duniya.
Ya ce kasashen duniya wadanda suka mallaki makaman nukiliya suna da wani nauyi na musamman dake rataye a wuyansu, ta hanyar daukar kwararan matakai, ciki har da yarjejeniyoyin da aka cimma a tarurrukan karawa juna sani game da shirin dakile bazuwar makaman nukiliyar wato (NPT) a takaice. (Ahmad Fagam)