Mr. Lajcak wanda ya yi wannan kira a jiya Litinin, a wani bangare na bikin ranar kasa da kasa ta kaucewa tashe tashen hankula, ya ce ya kamata MDD ta kara azama, wajen kaucewa amfani da karfi a muhimman sassan ayyukanta 3, wadanda suka hada da wanzar da zaman lafiya da tsaro, da kare hakkokin bil Adama, da kuma na samar da ci gaba. Ya ce batun shiga tsakani, na daga matakai managarta na kaucewa amfani da karfi a ayyukan majalissar.
Kaza lika Mr. Lajcak ya ce hakan dabara ce ta sanya bangarorin da ba sa ga maciji da juna komawa teburin shawarwari.
Da ya tabo babban taron majalissar karo 72 da ya kammala a makon jiya, jami'in ya ce kiraye kiraye da kasashe mambobin majalissar, da hukumomi tare da kungiyoyin kasa da kasa suka gabatar, na kaucewa amfani da karfin tuwo wajen wanzar da zaman lafiya na da ma'anar gaske.
Mr. Lajcak ya ce yanzu haka MDD ta shiga wani mataki na gudanar da gyare gyare ga tsarin ayyukanta, don haka yake kira ga masu ruwa da tsaki a ayyukan nata, da su rungumi kudurin nan na samar da yanayin zaman lafiya a sassan duniya ba tare da murda kwanji ba.
Wani kudurin MDD na shekarar 2007 ne dai ya tanaji kebe ranar 2 ga ko wane watan Oktoba, a matsayin ranar kasa da kasa ta kaucewa amfani da karfin tuwo, ranar da ta yi daidai da ranar haihuwar jagoran juyin juya halin nan dan kasar Indiya Mahatma Gandhi, wanda ya jagoranci gwagwarmayar samun 'yancin kan kasar, tare da kafa akidar kaucewa amfani da karfin tuwo.