in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe muhawarar babban taron MDD karo na 72
2017-09-26 10:20:23 cri
An rufe babbar muhawarar babban taron MDD karo na 72 da aka yi a hedkwatar Majalisar dake birnin New York a jiya Litinin, inda wakilan kasa da kasa suka bayyana ra'ayoyinsu kan yadda za a aiwatar da jadawalin neman dauwamammen ci gaba da yadda za a tunkari barazanar nukiliya da sauyin yanayi da yaki da ta'addabci da kuma warware matsalar 'yan gudun hijira da dai sauransu.

Taron da ya gudana tsakanin ranakun 19 da 25 ga watan nan, ya samu halartar shugabanni da wakilai na kasashe da gwamnatoci 196, inda kuma suka gabatar da jawabai.

Adadin wadanda suka gabatar da jawabi a taron na wannan karon ya kasance mafi yawa cikin shekaru 11 da suka gabata.

Bugu da kari, an yi taron shawarwari na musamman kan batun sauyin yanayi da kuma taron kwamitin sulhu na MDD kan gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya da dai sauransu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China