in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya na goyon-bayan dunkulewar Iraki a matsayin kasa daya
2017-09-29 11:36:17 cri
A kwanakin baya ne, Kurdawan Iraki suka kada kuri'ar raba gardama, a wani yunkuri na neman 'yancin kan yankin Kurdistan. Gwamnatin kasar Iraki tare da kasashen Turkiyya da Farisa wao Iran da wasu kasashe makwabta sun dauki matakai na mayar da martani. Har wa yau, Majalisar Dinkin Duniya, da Amurka, da Rasha da wasu kungiyoyin kasa da kasa sun nuna kin amincewa ga 'yancin da yankin Kurdawa ke nema, kana, suna goyon-bayan dinkewar Iraki a matsayin kasa daya tak.

Firaministan kasar Iraki, Haider al-Abadi ya ce, idan Kurdawan Iraki suna son ci gaba da yin shawarwari tare da gwamnatin Iraki, sai dai su yi fatali da sakamakon zaben raba gardamar, sannan su koma ga kundin tsarin mulkin kasar.

Gwamnatin Iraki ma tana nan tana kokarin samun goyon-baya daga kasashen duniya, domin nuna kin yarda da zaben raba gardamar da yankin Kurdawan Irakin ya gudanar.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China