in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iraki ta kwace muhimmin gari na karshe da ke hannun kungiyar IS a kasar
2017-08-28 11:20:00 cri

Wani babban jami'in sojin gwamnatin kasar Iraki ya bayyana a jiya Lahadi cewar, sojojin gwamnatin sun kwace garin Tal Afar, muhimmin gari na karshe da ke hannun kungiyar IS mai tsattsauran ra'ayi a kasar Iraki.

Laftana Janar Abdul-Amir Yarallah, kakakin hukumar dake jagorantar aikin yaki da kungiyar IS ta Iraki ya bayyana cikin sanarwar cewa, sojojin gwamnatin da dakarun sa-kai 'yan darikar 'yan Shi'a sun kame unguwanni biyu na karshe da ke arewacin garin Tal Afar jiya, lamarin da ya nuna cewa, yanzu an 'yantar da garin kwata kwata daga hannun mayakan IS.

A ranar 20 ga watan da muke ciki ne firaminitan Iraki Haider al-Abad ya sanar da kaddamar da yakin kwace garin na Tal Afar. Daga baya kuma, rundunar yaki da ta'addanci ta Iraki, da 'yan sandan kasar, da ma dakaru sa-kai na 'yan Shi'a suka dauki kwararan matakan soja daga sassa daban daban na birnin. Sojojin Iraki sun bayyana cewa, kafin a fara yakin, akwai 'yan kungiyar IS kimanin 2000 da ke zaune a ciki da wajen garin.

A waje daya kuma Laftana Janar Yarallah ya nuna cewa, a halin yanzu dai, dakaru 'yan kungiyar IS ke rike da yankin da ke da nisan kimanin kilomita 10 daga arewacin garin Tal Afar, kuma yanzu haka sojojin gwamnati sun nufi yankin.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China