in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Amurka ya gana da mataimakiyar firaministan majalisar gudanarwar Sin
2017-09-29 11:17:50 cri

Jiya Alhamis, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya gana da mataimakiyar firaministan majalisar gudanarwa ta kasar Sin Liu Yandong a fadar White House dake birnin Washington.D.C, fadar mulkin kasar Amurka.

Madam Liu ta je kasar Amurka ne, domin halartar taron karawa juna sani kan harkokin zaman takewar al'umma da al'adu a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka a karon farko.

A yayin ganawar tasu, Liu ta mika sakon fatan alheri na shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda ya aikewa shugaba Trump. Haka kuma, ta ce, kasar Sin tana maraba da ziyarar aikin da shugaba Trump zai kai kasar Sin cikin shekarar bana, bisa gayyatar da shugaban kasar Sin ya yi masa, kuma ana saran cimma sakamako mai gamsarwa bisa ziyararsa a kasar Sin.

Daga bisani kuma, Madam Liu ta bayyana cewa, an cimma nasarori da dama a yayin taron da ake yi, bisa kokarin da kasashen biyu suka yi cikin hadin gwiwa. Kuma ana fatan ci gaba da habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannonin samar da ilmi, kimiyya da fasaha da kuma kiwon lafiya da dai sauran makamantansu.

A nasa bangaren, shugaba Trump ya mika sakon fatan alheri ga shugaba Xi Jinping, yana mai cewa, tabbas ne za a habaka mu'amalar al'adu da al'ummomin kasashen biyu sakamakon ziyararsa a kasar Sin.

Bugu da kari, yana fatan za a ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu bisa fannoni daban daban a nan gaba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China