A yayin ganawar, Yang Jiechi ya yi nuni da cewa, tabbatar da raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka ya dace da moriyar kasashen biyu, kuma shi ne burin kasashen duniya.
A cewar Yang, a bana ne ake sa ran shugaban kasar Amurka Donald Trump zai kawo ziyara kasar Sin bisa gayyatar takwaransa na kasar Sin Xi Jinping. kasar Sin tana fatan hada kai tare da kasar Amurka don ganin ganawar ta yi nasara.
A nasa bangare, Tillerson ya bayyana cewa, shugaba Trump yana begen ziyarar da zai kai kasar Sin a bana, yana kuma son tsara makomar dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka tare da shugaban kasar Sin Xi Jinping. Kasar Amurka tana fatan hada kai tare da kasar Sin a fannin musayar ra'ayi a fannin zamantakewar al'umma, da al'adu, a tsakanin kasashen biyu zagaye na farko, da tattaunawa kan dokoki da tsaron yanar gizo, da zurfafa hadin gwiwa a dukkan fannoni, da kara yin mu'amala da juna kan manyan batutuwan duniya da yankuna, bisa tushen musayar ra'ayi a fannonin harkokin waje da tattalin arziki a tsakaninsu. Ana fatan sakamakon da za a samu a yayin ganawar shugaba Trump da shugaba Xi a kasar Sin za ta sa kaimi ga samun bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata. (Zainab)