in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta dauki matakan da suka dace na kare muradunta
2017-08-21 19:34:29 cri

Ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin ta bayyana a yau Litinin ce, kasar za ta dauki dukkan matakan da suka wajaba don ganin ta kare muradunta kamar yadda doka ta tanada, domin mayar da martani ga binciken da Amurka ta gudanar game da harkokin cinikayyar Sin, lamarin da ya haifar zaman tankiya tsakanin kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya.

Mai Magana da yawun ma'aikatar cinikayyar kasar ta Sin wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, ya ce kasar Sin za ta sanya ido kan wannan batu, sai dai kasar Sin ba ta bayyana wadannan irin matakai za ta dauka ba.

A ranar Jumma'ar da ta gabata ce wakilin cinikayya kasar Amurka Robert Lightjizer ya gudanar da bincike a hukumance game da ayyukan mallakar fasahar kasar Sin, ayyukan da ba safai ake amfani da su bisa doka ba. Sai dai Amurkar ba ta damu game da illar da hakan ka iya yiwa hadin gwiwar sassan biyu ta fannin cinikayya ba.

An taba amfani da sashi na 301 a shekarun 1980 da farko shekarun 1990, matakin da ya baiwa Amurka damar kakaba haraji ko wasu takunkuman cinikayya kan kasashen ketare. Amma kuma ba ta taba amfani da tsoffin dokokin cinikayyar ba, tun lokacin da aka kafa kungiyar cinikayya ta duniya a 1995.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China