in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Maitamakiyar firaministar kasar Sin za ta ziyarci Amurka
2017-09-25 20:14:33 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana a yau Litinin cewa, bisa ra'ayi daya da aka cimma tsakanin shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump, an shirya gudanar da taron musayar ra'ayi tsakanin Sin da Amurka ta fuskar zamantakewar al'umma, da al'adu a karo na farko, taron da zai gudana a ranar 28 ga watan nan a birnin Washington na kasar Amurka.

Ana sa ran mataimakiyar firaministar kasar Sin Liu Yandong, da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Rex Tillerson ne za su ja ragamar taron. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China