in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron karawa juna sani kan harkokin zaman takewar al'umma da al'adu a tsakanin Sin da Amurka karo na farko
2017-09-29 11:16:55 cri
A jiya Alhamis ne, aka bude taron karawa juna sani game da harkokin zaman takewar al'umma da al'adu a tsakanin Sin da Amurka karo na farko a birnin Washington.D.C, fadar mulkin kasar Amurka. Mataimakiyar firaministar kasar Sin Liu Yandong ta halarci taron da suka jagoranta da ministan harkokin wajen kasar Amurka Rex Tillerson.

A yayin taron, madam Liu ta bayyana cewa, an cimma sakamako da dama a fannin mu'amalar al'adu a tsakanin al'ummomin kasashen biyu, bisa kokarin da shugabannin kasashen biyu suka yi. Lamarin da ya ba da gudummawa sosai kan raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Haka kuma, an fidda wata sanarwar hadin gwiwa a yayin taron karawa juna sani kan harkokin zaman takewar al'umma da al'adu a tsakanin Sin da Amurka karo na farko. An kuma amince a zartas da wani jadawalin mu'amalar zaman takewar al'umma da al'adu a tsakanin Sin da Amurka, domin aiwatar da shirye-shirye guda 130 da abin ya shafa.

A nasa bangare, Mr. Tillerson ya ce, ma'amalar dake tsakanin al'ummomin kasar Sin da Amurka ta karu sosai cikin shekarun baya bayan nan, kuma, kasar Amurka tana son ci gaba da habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a wannan fanni, tare da aiwatar da sakamakon taron yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China