A yau Laraba ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a nan Beijing cewa, kwanan baya, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin Yang Jiechi ya gana da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Rex Tillerson a birnin Washington na kasar Amurka. Kuma a yayin ganawar tasu, Yang Jiechi ya yi nuni da cewa, a bana ne ake sa ran shugaban kasar Amurka Donald Trump zai gudanar da ziyara a kasar Sin bisa gayyatar takwaransa na kasar Sin Xi Jinping.
Mr. Yang ya ce kasar Sin na fatan ci gaba da kokari tare da bangaren Amurka, wajen ganin an samu sakamako mai gamsarwa a ziyarar ta shugaba Trump.
A nasa bangaren kuwa, mista Tillerson cewa ya yi, Amurka na fatan ci gaba da tuntubar kasar Sin, domin tabbatar da cimma sakamakon da ake fata a ziyarar ta shugaba Trump. (Tasallah Yuan)