Ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin ta bayyana damuwa game da sabuwar dokar da shugaba Trump na kasar Amurka ya sanya hannu a kai, wadda ke umartar wakilin harkokin cinikayyar Amurka da ya bincike zargin da Amurkar ke yi wa kasar Sin game da ayyukanta na mallakar fasaha.
Wata sanarwa da ma'aikatar ta wallafa a shafinta na Intanet, ta bayyana cewa, idan har bangaren Amurka ya gaza mutunta shaida na zahiri da dokokin cinikayya na kasa da kasa, kana ta yi gaban kanta wajen daukar matakan da za su lalata dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu. Hakika ita ma kasar Sin za ta dauki matakan da suka dace don kare 'yanci da kuma muradunta. (Ibrahim)