in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sin zai halarci babbar muhawarar MDD
2017-09-11 20:02:23 cri

Yau Litinin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya sanar da cewa, za a fara babban taron MDD karo na 72 a ranar 12 ga watan nan da muke ciki, a babban zauren MDD da ke birnin New York na kasar Amurka, taron da zai kunshi babbar muhawara ta ranar 19 ga wata. Ya ce ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, zai jagoranci tawagar kasar domin halartar babbar muhawarar, inda zai yi cikakken bayani kan matsayin kasar Sin dangane da halin da ake ciki a duniya, da al'amuran kasa da kasa da na shiyya-shiyya, zai kuma bayyana aniyar kasar Sin wajen hada kai da kasashe mambobin MDD a fannonin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, tare da samun ci gaba da wadata. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China