Jiya Talata ne, Liu Jieyi, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya bayyana matsayin kasar Sin yayin wata muhawarar kwamitin sulhu dangane da batun ayyukan kiyaye zaman lafiya, inda ya ce, kasar Sin na ganin cewa, dole ne MDD ta hada matakai 4 na ayyukan kiyaye zaman lafiya baki daya, wato yin rigakafin barkewar rikici, kwantar da kura, kiyaye zaman lafiya, da samun dawwamammen zaman lafiya.
Mista Liu ya nuna cewa, kasar Sin na fatan MDD da kungiyar tarayyar Afirka wato AU za su zurfafa hadin gwiwa a tsakaninsu a fannonin yin rigakafin barkewar rikici, daidaita rikici, aikin farfadowa bayan rikici da dai sauransu. Kasar Sin na mara wa MDD baya wajen yin la'akari da shirin Afirka na tattara kudin gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya da kansu, da goyon bayan AU a fannin kiyaye zaman lafiya da kansu, da taimaka musu da kudi. Kasar Sin tana fatan MDD za ta mara wa kasashen Afirka baya wajen gaggauta bunkasa tattalin arziki, a kokarin magance matsalolin da ta haddasa rikici daga tushe. (Tasallah Yuan)