Yang Jiechi ya ce kasar Sin ta dauki rawar da MDD ke takawa a harkokin kasashen duniya da matukar muhimmanci, sannan tana goyon bayan zauren majalisar wajen aiwatar da jerin muradun ci gaba masu dorewa da ake son cimmawa daga nan zuwa shekarar 2030.
Shi ma a nasa bangaren, Miroslav Lajcak ya yabawa rawar da kasar Sin ke takawa a kan harkokin da suka shafi majalisar, yana mai cewa a shirye yake ya kara inganta hadin kai da kasar.
An zabi Miroslav Lajcak ne a ranar 31 ga watan Mayun bana a matsayin shugaban zaure na 72 na MDD, inda zai shafe tsawon shekara guda kan mukamin.
Lajcak zai maye gurbin Shugaba mai ci Peter Thomson, a zaman zauren majalisar da za a yi a watan Satumba mai zuwa. (Fa'iza Mustapha)