Mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao ya bayyana kudurin kasarsa na zurfafa hadin gwiwa da MDD, a wani mataki na tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a duniya.
Li wanda ya bayyana hakan yayin ganawarsa da shugaban babban taron MDD karo na 72 Miroslav Lajcak, ya ce kasar Sin za ta goyi bayan rawar da MDD ke takawa a harkokin kasa da kasa, kana kasar Sin ta fatan MDD za ta cimma nasarori wajen aiwatar da ajandar samun ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030.
A nasa jawabin Lajcak ya ce yana fatan kasar Sin za ta taka rawar da ta dace wajen goyon bayan babban taron na MDD.
A ranar 31 ga watan Mayun wannan shekara ne aka zabi Lajcak bisa wannan mukami, inda zai maye gurbin shugaban na wannan karo Peter Thomson, yayin zaman babban taron majalisar na wannan Satumban wannan shekara.(Ibrahim)