Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana yau Talata 4 ga wata ce, yayin da kasar Sin ke rike da mukamin shugabancin kwamitin sulhun MDD na watan Yulin bana, za ta sauke mauyin dake wuyanta yadda ya kamata, tare da kuma dukufa wajen warware matsalolin Afirka da na gabas ta tsakiya ta hanyar kiran wasu taruruka da ma gudanar da babbar muhawara.
Geng Shuang ya furta cewa, kwanan nan zaunannen wakilin kasar Sin da ke MDD Liu Jieyi, ya shugabanci shawarwarin kwamitin sulhu, inda aka zartas da shirin aiki na watan Yuli. Geng ya kara da cewa, a wannan watan da muke ciki, kwamitin sulhun zai kira taruka kusan 30, don tattaunawa kan batutuwan Sham, da Yemen, da Iraki, da Lebanon, kana da batutuwan Sudan ta Kudu, da Congo Kinshasa, da Burundi, da ma aikin ofishin MDD da ke yammacin Afirka da yankin Sahel, da dai sauransu.(Kande Gao)