in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya halarci bikin bude taron kungiyar 'yan sanda ta kasa da kasa
2017-09-26 15:59:30 cri
Yau ne, aka bude babban taron kungiyar 'yan sandan kasa da kasa a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda wakilan hukumonin da abin ya shafa daga kasashe kimanin guda 158 suka halarci wannan taro.

A jawabinsa yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, cikin shekaru biyar masu zuwa, gwamnatin kasar Sin za ta kara goyon bayan da take baiwa kungiyar 'yan sanda ta kasa da kasa, da kuma taimaka wa kungiyar wajen gudanar da aikace-aikace cikin hadin gwiwa sau uku a ko wace shekara a fannonin yaki da ta'addanci da kuma yaki da masu aikata laifuffuka ta yanar gizo da dai sauransu .

Ban da haka kuma, za ta taimaka wajen inganta kwarewar kungiyar wajen gudanar da ayyukanta bisa dokoki yadda ya kamata, ta yadda za a karfafa tasirin kungiyar a duk fadin duniya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China