A jiya Laraba ne, a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin shugaba Xi Jinping na kasar ta Sin ya karbi takardun kama aiki na jakadun kasashe 14 wadanda za su wakilci kasashensu a nan kasar Sin.
A jawabinsa shugaba Xi ya yiwa sabbin jakadun maraba da zuwa kasar Sin, kana ya bukace su da su mika sakonsa na gaisuwarsa da fatan alheri ga shugabanni da kuma al'ummomin kasashensu. Shugaba Xi ya kuma yi dogon bayani game da kyakkyawar alakar dake tsakanin Sin da kasashen nasu.
Ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da karfafa alaka da tsarin nan na mutunta juna tsakanin sassan biyu a fannonin siyasa, da musaya, ta yadda za a daga matsayin wannan alaka.
A nasu bangaren sabbin jakadun da suka hada da na kasashe Najeriya, da Senegal, da Burundi, da Uganda da Kenya da Gabon da sauransu, su ma sun isar da sakonnin fatan alherin shugabanninsu ga shugaba Xi. Sun kuma bayyana cewa, kasashensu na martaba kyakkyawar dangantakar dake tsakaninsu da kasar Sin, da ma al'ummomin kasashen. Suna fatan cewa, za su shiga shawarar nan ta "Ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar, tare da zaurfafa hadin gwiwar moriyar juna da kasar Sin, (Ibrahim)