Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar hadin gwiwa kasa da kasa game da batun yaki da kwararowar hamada. Shugaba Xi wanda ya yi wannan tsokaci cikin wata wasika da ya aike ta taya murnar bude taron tattaunawa, na masu ruwa da tsaki game da yaki da kwararar hamada mai taken COP13, ya bayyana yawaitar hamada a matsayin babban kalubale ga daukacin al'ummar duniya.
An dai bude taron na COP13 karo na 13, karkashin shirin yaki da kwararar hamada na MDD ko UNCCD a takaice, a ranar Litinin din nan a birnin Ordos dake Mongolia ta cikin gida mai cin gashin kanta, dake arewa maso gabashin kasar Sin. (Saminu Hassan)