Da yake tofa albarkacin bakin sa, shugaba Xi ya bayyana cewa, Sin da Amurka na da muradu makamanta, sun kuma samu ci gaba a fannonin hadin gwiwa a dukkanin bangarori.
Xi Jinping ya ce yana farin cikin ganin ya ci gaba da tattaunawa akai akai da tsagin Amurka, game da batutuwan da ke jawo hankalin sassan biyu. Ya ce kasar sa na dora muhimmancin gaske game da ziyarar Mr. Trump, yana mai fatan za su ci gaba da gudanar da tsare tsare, da za su tabbatar da nasarar ziyarar, tare da bude sabuwar kofa, ta raya dangantakar sassan biyu yadda ya kamata.
A nasa bangare kuwa, shugaban na Amurka cewa ya yi, yana da burin gudanar da ziyarar da ake shiryawa, tare da fadada kawance tsakanin kasar sa da Sin.
Bugu da kari shugabannin biyu sun yi musayar ra'ayoyi, don gane da halin da ake ciki a zirin koriya. (Saminu Alhassan)