Mai magana da yawun rundunar sojojin tarayyar Najeriya, kanar Onyema Nwachukwu ya ce, an dawo da dukkanin yankunan da mayakan Boko Haram suka kwace a baya hannun sojojin gwamnatin Najeriya.
Kana, Nwachukwu ya karyata rahoton dake cewa wai har yanzu akwai kananan hukumomi 27 a jihar Borno wadanda ke hannun Boko Haram.
Ya kara da cewa, matakan soja da aka dauka na kafa rundunar yaki da Boko Haram ta Lafiya Dole, sun taka muhimmiyar rawa wajen samun galaba kan mayakan, haka kuma sun kawar da mayakan na Boko Haram daga babbar matattararsu dake dajin Sambisa gami hedikwatar da suke yada da'awar kungiyar a garin Alagarno.(Murtala Zhang)