in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayakan Boko Haram 6 sun mika wuya ga Jami'an tsaro a Nijeriya
2017-09-12 10:30:56 cri
Hukumar wanzar da tsaro da zaman lafiya ta Nijeriya wato NSCDC, ta ce mayakan Boko Haram 6 sun mika wuya ga jami'an tsaro a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Kakakin hukumar James Bulus ya bayyana a jiya cewa, mayakan da suka tuba, sun ajiye makamansu ne biyo bayan tsananta ayyukan tsaro a yankin arewa maso gabashin kasar cikin makonnin baya-bayan nan.

Ana sa ran za a sauya akidar tsoffin 'yan tawayen da gyara musu halayya tare da sake shigar da su cikin al'umma, wadanda shirye-shirye ne da gwamnatin kasar ta tsara da nufin karfafawa karin mayakan Boko Haram gwiwar ajiye makamansu.

Wani mai sharhi kan al'amuran tsaro a kasar, ya ce wannan ci gaba na kara tabbatar da nasarori da Nijeriya ke samu daga dabarun da ta dauka na yaki da ta'addanci da kawo karshen muggan ayyukan Boko Haram da suka shafe shekaru, al'amarin da ya zama babban kalubalen tsaro a yankin yammacin Afrika. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China