A ranakun 24 da 25 ga watan nan da muke ciki, mayakan Boko Haram sun kai hare-hare a garuruwa biyu dake yankin Arewa mai nisa na kasar Kamaru, yankin ke kusa da kan iyakarta da Nijeriya.
Baya ga mutane 18 da suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren, mayakan sun kuma yi garkuwa da wasu mutane 8, yayin da suka kone gidaje sama da 30.
Kimanin shekaru 10 ke nan da fara ayyukan Kungiyar Boko Haram, kuma cikin wadannan shekaru, kungiyar ta kai hare-hare da dama a Nijeriya da kasashen makwabtanta, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane masu tarin yawa.
A cikin watan Maris din shekarar 2015 ne, kungiyar Boko Haram ta sanar da mubaya'arta ga kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS.
A kuma watan Yulin bara ne, Nijeriya da kasashen makwabtanta da suka hada da Kamaru da Nijer da Chadi, suka kafa wata rundunar soja ta hadin gwiwa, domin yaki da kungiyar Boko Haram.
Duk da cewa rundunar ta cimma nasarar dakile wasu aikace-aikacen Boko Haram, har yanzu kungiyar ba ta daina kai hare-hare a yankunan. (Maryam)