Da take jawabi yayin wani taron yini biyu kan yadda rikicin ke shafar bambancin jinsi a birnin Yola jihar Adamawa, mataimakiyar wakilin hukumar a Nijeriya da kuma kungiyar ECOWAS Bridgette Mukanga-Eno, ta ce sama da yara 8,000 aka yi kiyasin kungiyar Boko Haram ta horar tare da yin amfani da su.
Jami'ar ta kara da cewa, sama da mata da 'yan mata 7,000 ne boko haram ta ci zarafinsu, ciki har da aurensu bisa tilas.
A cewarta, mata da 'yan mata da Boko Haram ta saki, da galibi ke da yara, za su fuskanci kalubale ba kadai na nuna musu kyama da kin mu'amala da su ba, har da cin zarafi a wasu al'ummomin.
Bridgette Eno ta shaidawa mahalarta taron cewa, rahoton cin zarafin mata a sansanoni da yankunan da suka ba 'yan gudun hijira mafaka, abu ne mai matukar tada hankali, domin akwai rahoton batutuwan cin zarafi da fyade, kuma cikin masu aikata laifin har da jami'an tsaro.
Har ila yau, ta ce baya ga take hakkin dan Adam, 'yan gudun hijira ba sa iya samun gata ta fuskar shari'a da zai taimaka musu gudanar da harkokinsu na yau da kullum. (Fa'iza Mustapha)