in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin Nijeriya ta lashi takobin murkushe dukkan mayakan Boko Haram
2017-09-02 12:30:00 cri
Duk da hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kai wa mutane masu rauni a yankin arewa maso gabashin Nijeriya, Rundunar sojin kasar ta ce babban aikin dake gabanta a yanzu shi ne, murkushe ragowar 'ya'yan kungiyar.

Cikin wata sanarwa da ta shiga hannun kamfanin dillancin labarai na Xinhua jiya a Lagos, babban hafsan sojin Nijeriya Lt-Janar Tukur Buratai ya yabawa dakarun bisa murkushe manyan kwamandojin kungiyar 5 da suka yi.

Ya kuma bayyana gamsuwa da karsashi da jajircewar dakarun, na tabbatar da kama shugaban kungiyar Abubakar Shekau a raye ko a mace bisa umarnin da ya bayar, wanda kawo yanzu, ba a kai ga cikawa ba.

A ranar 21 ga watan Yulin da ya gabata ne Babban hafsan sojin ya ba kwamadan yaki da kungiyar Manjo-Janar Ibrahim Attahiru, wa'adin kwanaki 40 na kama shugaban kungiyar, inda wa'adin ya cika a ranar 30 ga watan Augustan da ya gabata.

Tukur Buratai ya ce shugabannin kungiyar 5 da dakarun suka kawar a baya-bayan nan makusanta ne kuma na hannun daman jagoran kungiyar.

Har ila yau, ya ce cikin wancan lokaci da aka dibar, an murkushe mayakan kungiyar 82, ya na mai cewa, kwamnadan dake yakin na gab da cika umarnin.

Bugu da kari, babban Hafsan ya ce Kwamandan ya nemi a kara tsawaita wa'adin, kuma tuni aka amince da bukatar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China