in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani jigo a kungiyar Boko Haram ya mika wuya
2017-08-29 09:52:00 cri
Rundunar sojan Najeriya ta tabbatar a jiya Litinin cewa, daya daga cikin jiga-jigan kungiyar Boko Haram ya mika kansa ga dakarun kasar dake aikin kakkabe mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.

Rahotanni na cewa, a lokacin da kwamandan kungiyar mai suna Auwal Ismaaela ya mika wuya ya kuma amsa cewa, yana daga cikin wadanda suka jagoranci sace 'yan matan sakandaren nan na garin Chibok sama da 200 dake jihar Borno.

Mika wuyan da Ismaaela ya yi ga dakarun, ya biyo bayan kara kaimin da suke yi na kakkabe gyauron kungiyar 'yan ta'addan a Najeriya.

Mayakan na Boko Haram dai na amfani da kananan yara, musamman 'yan mata, wajen tayar da bama-bamai a sassan kasar daban-daban.

A ranar Talatar da ta gabata ce, asusun tallafawa kananan yara na MDD (UNICEF) ya bayyana damuwa game da yadda ake samun karuwar amfani da yara a matsayin bama-bamai. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China