in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sanda 5 sun jikkata a harin kunar bakin wake a arewa maso gabashin Najeriya
2017-08-24 09:30:34 cri
A kalla 'yan sanda 5 ne suka samu munanan raunuka a sanadiyyar harin kunar bakin wake da aka kaddamar da yammacin ranar Laraba wanda ake zargin mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram da kaddamarwa a jahar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya.

Wata majiya daga hukumar tsaron kasar da ta nemi a sakaye sunanta, ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, maharan biyu sun kaddamar da harin ne a kauyen Muna dake wajen birnin Maiduguri, babban birnin jahar Borno.

Majiyar ta ce, 'yan kunar bakin waken sun shirya kaddamar da harin ne kan wata motar 'yan sanda, amma 'yan sandan sun tsallake rijiya da baya, kasancewar basu mutu ba a sanadiyyar harin.

Ahmed Satomi, shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jahar, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, jami'an tsaro sun yi nasarar harbe dan kunar bakin waken guda daya, lamarin da ya hana shi tayar da boma bomai dake daure a jikinsa.

Satomi ya ce, maharin na biyu ya fito ne daga cikin wata kasuwa dake kusa da inda lamarin ya faru, inda yayi kokarin kaddamar da hari kan ma'aikatan hukumar agajin gaggawa dake kokarin kwashe wadanda suka jikkata a harin da aka kaddamar na farko.

Tun daga watan Yuli, hare haren kunar bakin wake na cigaba da karuwa a Maiduguri, birni mafi girma a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

Kungiyar Boko Haram ta sha daukar alhakin kaddamar da mafi yawan hare haren ta'addanci a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, a baya bayan nan kungiyar ta yi ikirarin yin garkuwa da wasu ma'aikatan jami'ar Maiduguri dake aikin binciken mai a tafkin Chadi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China