Kasashen Sin da Kenya, sun rattaba hannu a jiya Alhamis, kan wata yarjejeniyar kawar da matsalar biyan haraji sau biyu, wadda ke da nufin inganta huldar kasuwanci a tsakaninsu.
Sakataren Baitul Malin Kenya Henry Rotich, ya shaida wa manema labarai a Nairobi cewa, yarjejeniyar za ta samar da tabbaci ga masu biyan haraji, kan harajin da ake biya na kudaden shiga da za a samu daga ko wace kasa a cikinsu. (Fa'iza Mustapha)