Mista Kenyatta ya shedawa 'yan jaridu a Nairobi cewa, bai ga dalilin da zai sa sa kotun daukar wannan mataki na soke zaben da miliyoyin al'ummar Kenya suka amince da aiwatar da shi ba tare da wasu kwararan hujjoji ba.
Ita dai kotun kolin kasar dake zamanta a birnin Nairobi ta amince da soke sakamakon zaben wanda ya sake baiwa shugaba Kenyatta nasara da kashi 54 cikin 100 a kan abokin hamayyarsa Raila Odinga, wanda ya samu kashi 44 bisa 100 na yawan kuri'u a zaben da aka kada a watan jiya.(Ahmad Fagam)