in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadakar jam'iyyun adawa a Kenya ta kaddamar da gangamin neman korar wasu jami'an hukumar zabe
2017-09-18 09:49:25 cri
Shugaban hadakar jam'iyyun adawa ta kasar Kenya Raila Odinga, ya kaddamar da wani gangamin a jiya, da nufin samar da sauyi a hukumar zaben kasar, kafin ya shiga sabon zaben shugaban kasar da aka shirya gudanarwa a ranar 17 ga watan Oktoba.

Shugaban na NASA, ya ce zaben da za a sake yi a watan gobe, ba zai kasance sahihi ba, muddun wasu jam'ai sun ci gaba da kasasncewa a hukumar zaben kasar, wadanda yake zargi da taimakawa magudin zaben ranar 8 ga watan Augusta.

Raila Odinga ya shaidawa wani taron manema labarai a Nairobi cewa, sun kaddamar da gangamin ne domin nuna adawa da duk wani zabe da hukumar za ta shirya, inda ya ce za su zagaye fadin kasar domin wayar da kan al'umma game da hukumar.

Shugaban 'yan adawar mai shekaru 72, wanda ya samu nasara a karar da ya shigar kotun kolin kasar da ta soke zaben shugaban kasa na ranar 8 ga watan Augusta tare da soke nasarar zaben shugaba mai ci Uhuru Kenyatta, ya ce yayin gangamin, za su zagaya fadin kasar domin yi wa magoya bayansu bayanin dalilin da ya sanya ba za su amince hukumar za ta gudanar da sahihin zabe ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China