in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan ganin an samu masalaha tsakanin bangarorin Syria
2016-12-27 20:08:37 cri
Dangane da sabon zagayen shawarwari game da kasar Syria da zai gudana, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Madam Hua Chunying ta bayyana a wajen taron manema labaru da aka kira yau a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin tana maraba da duk wani kokarin na neman maido da shawarwari tsakanin bangarorin kasar Syria cikin hanzari, haka kuma kasar na fatan ganin bangarori daban daban na Syria sun cimma matsayi daya, wanda zai biya bukatun kowa.

Jami'ar ta nanata cewa, shawarwari ita ce hanya daya taka da za a iya bi don warware batun Syria. Hakan a cewar jami'ar shi ne ra'ayin bai daya na gamayyar kasa da kasa, wanda ya kasance alkiblar da bangarori daban daban suke kokarin bi kan batun. Ta ce ya kamata bangarorin kasar Syria su yi kokarin tabbatar da tsagaita bude wuta tsakaninsu, wanda zai zama nasara ta farko, matakin da zai kai ga tabbatar da yunkurin daidaita batun na Syria ta hanyar siyasa.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China