Mamban ofishin siyasar kwamitin tsakiyar JKS Liu Qibao ya halarci taron, inda ya ba da jawabi, yana mai bayyana cewa, ya kamata ofisoshin yada labarai dake kasashen ketare su dukufa wajen bayyana manufofin kasar Sin kan gudanar da ayyukan kasa, da kuma yada labarai game da jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da tsarin gurguzu na musamman da kasar Sin take amfani da shi, ta yadda za a ba da gudummawa wajen gudanar da taron wakilan JKS karo na 19 cikin yanayi mai armashi. (Maryam)