in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jagororin JKS sun yi kiran da a ci gaba da yaki da cin hanci
2016-12-28 19:09:08 cri
Shugabannin JKS sun ba da umarnin kara zage damtse a yakin da ake yi da cin hanci da rashawa, a wani mataki na tsarkake tsarin siyasar kasar.

Wannan kiran na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka bayar a karshen taron hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS da ya gudana a yau Laraba.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, wajibi a kawo karshen matsalar cin hanci da karbar rashawa da ke kokarin zama karfen kafa a sabuwar shekarar 2017 da za mu shiga.

Babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS Xi Jinping ne ya jagoranci taron.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China