Masanan ketare: Yadda JKS ta dauki kwararan matakai wajen tafiyar da harkokin jam'iyyar yana da muhimmanci
A yayin cikakken zama karo na 6 na kwamitin tsakiyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, an tsara shiri kan daukar kwararran matakai wajen tafiyar da harkokin jam'iyyar a dukkan fannoni, inda kuma aka duba da zartas da ka'idoji game da gudanar da harkokin jam'iyyar da kuma sa ido a kai a cikin sabon yanayin da ake ciki. Game da haka, wasu masanan kasashen ketare sun bayyana cewa, daukar kwararran matakai wajen tafiyar da harkokin jam'iyyar a sabon yanayin da ake ciki, yana da ma'ana sosai, ba ma kawai zai amfanarwa kasar Sin ba ne, har ma zai kawo cin gajiya ga duniya baki daya.
Shehu malami na jami'ar People's Friendship ta kasar Rasha, Yury Tavrovsky, yana mai cewa, karfafa ladabtarwa a cikin jam'iyyar, da kyautata tsarin gudanar da harkoki, da kuma kawar da cin hanci da rashawa, sun kasance kudurori da suka wajaba a dauka a yayin zaman taro na wannan karo.
A nasa bangaren, malami a fannin tatalin arzikin duniya na jami'ar Nairobi, kuma tsohon mataimakin ministan zirga-zirgar kasar Kenya, Garrishon Ikiara ya bayyana cewa, sanarwar da aka bayar a yayin zaman taron ta nuna niyyar jam'iyyar Kwaminis ta Sin na jagorancin jama'ar kasar wajen inganta tattalin arziki da zamantakewar al'umma. (Bilkisu)