Taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19, zai yi duba na tsanaki game da ayyukan jam'iyyar cikin shekaru biyar da suka gabata, ya kuma kididdige darussa da jam'iyyar ta gamu da su, da kwarewa da ta dada samu, wajen hada kan al'ummomin kasar Sin a kokarin bunkasa ra'ayin gurguzu mai yanayi na musamman na kasar Sin, karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tun daga taron ta na 18.
Kaza lika za a nazarci halin da ake ciki a gida da waje, a kuma maida hankali ga bukatun da ake da su, dangane da kara gina jam'iyyar da kasar Sin yadda ya kamata, da kuma cimma muradun al'ummar kasar baki daya.
Taron zai kuma fidda ka'idoji da tsare tsare, domin biyan bukatun dake bijirowa akai akai.
Za kuma a gudanar da zaben wakilan kwamitin tsakiya na jam'iyyar, da mambobin babban kwamitin ladabtarwa da sanya ido, kamar dai yadda aka bayyana yayin taron da ya gabata.