in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a fara zaben wakilan da za su halarci cikakken zaman taron wakilan JKS karo na 19
2016-11-09 14:01:54 cri
A yayin cikakken zaman taro karo na 6 na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 18, an tsai da kudurin cewa, za a kira cikakken zaman taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 19 a watanni 6 na karshen shekarar 2017. Wannan ya sa a kwanan baya, kwamitin tsakiyar JKS ya fidda sanarwa game da zaben wakilan da za su halarci cikakken zaman taron, inda ya tsara manufofin gudanarwa da wannan aiki a dukkan fannoni. Haka kuma, sashen tsare-tsare na kwamitin tsakiya na JKS ya shirya taro domin yin cikakken bayani kan yadda za a gudanar da wadannan ayyuka a nan gaba. (Maryam)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China