in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta fadada harkokin kasuwanci ta intanet domin inganta cinikayya da kasashen ketare
2017-09-21 09:40:28 cri

Kasar Sin za ta kara kafa yankunan kasuwanci ta intanet domin karar saukaka cinikayya da nufin inganta takararta a duniya.

An dauki wannan mataki ne yayin taron majalisar gudanarwar kasar da ya gudana jiya karkashin shugabancin Firaminista Li Keqiang.

Taron ya yanke shawarar fadada nasarorin da yankunan cinikayya ta kafar intanet da kasashen ketare, zuwa wasu birane dake da ingantattun kayayyakin more rayuwa, wadanda ke da tsarin cinikayya mai karfi tare da damammaki a fadin kasar.

Majalisar gudanarwar kasar ce ta samar da wannan shiri a Hangzhou cikin shekarar 2015, kafin a farkon 2016 a fadada zuwa wasu karin birane 12 ciki har da Shanghai da Tianjin da Chongqing.

Kididdigar ma'aikatar kasuwanci ta kasar ta nuna cewa, kawo shekarar 2016, shirin na cinikayya ta intanet na kasar Sin ya mamaye kasashe da yankuna 220 na duniya, inda ake samun ribar kudin Sin yuan triliyan 5.85 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 891.

Yawan kudaden cinikayya da kasashen ketare bisa wannan shiri a yankuna 13 da aka fara aiwatar da shi, ya kai Yuan billiyan 163.7 a cikin shekarar 2016, abun da ya karu da sama da kashi dari bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2015.

Har ila yau karkashin shirin, an kafa dandalin cinikayya sama da 400 tare da kamfanonin 20,000 a yankunan da aka fara aiwatar da shi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China