A yau ne taron kwamitin tsakiya na hukumar kula da harkokin siyasa na JKS ya bayyana cewa, kasar Sin za ta aiwatar da ayyukan raya tattalin arzikinta a rubu'i na biyu na wannan shekara, duk da ci gaba da kuma daidaito da aka samu.
Taron wanda shugaba Xi Jinping, kana babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS na jagoranta, ya jaddada cewa, a farkon wannan shekara, kasar Sin za ta mayar da hankali wajen aiwatar da managartan manufofi da ingantatun manufofin kudi wadanda za su taimakawa wajen yiwa bangaren samar da kayayyakin gyaran fuska.
Wata sanarwa da aka fitar bayan taron, ya bayyana cewa, kamata ya yi a kara daukar matakai na tabbatar da ci gaban tattalin arziki yadda ya kamata, da ciyar da yiwa sashen samar da kayayyaki gyaran fuska gaba, da kiyaye fadawa hadarin kudi.(Ibrahim Yaya)