Wani rahoton kididdiga da aka fitar a Jumma'ar nan, ya nuna cewa ya zuwa watan Yunin da ya shude, yawan masu amfani da yanar gizo a kasar Sin ya kai mutum miliyan 751, adadin da ya karu da kaso 2.7 bisa dari tsakanin karshen shekarar bara ya zuwa watan na Yuni.
Rahoton ya ce mutane miliyan 724 na amfani ne da wayoyin salula domin shiga yanar gizo, adadin da ya kai kusan kaso 96.3 bisa dari na daukacin masu amfani da yanar gizo a kasar.(Saminu)