Hukumar kididdiga ta kasar Sin NBS, ta ce sashen sarrafa kayan masana'antu na kasar Sin ya samu ci gaba a watan Yuli, inda tagomashin sashen ke ci gaba da karuwa har watanni 12 a jere ya zuwa watan na Yuli.
Wasu alkaluma da NBS ta fitar ta ce alkaluman kidayar hajojin da ake saya daga masana'antun sun kai ga kaso 51.4 a watan Yuli.
Mizanin da ake amfani da shi na nuna karuwar fanni da zarar kason ya haura 50 bisa dari.