in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CPI na Sin ya karu da kashi 1.4 bisa dari a watan Yuli
2017-08-10 12:08:17 cri
Hukumar kididdigar kasar Sin ta fidda rahoto a jiya, wanda ke cewa a watan Yuli, alkaluman awon sauyin tsadar kayayyaki da na hidimomi cikin wani kayyadadden lokaci wato CPI na kasar Sin ya karu, da kashi 1.4 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.

Haka kuma, adadin ya ragu da kashi 0.1 bisa dari idan aka kwatanta da na watan Yunin bana.

Kuma bisa kididdigar da aka yi, an ce, cikin manyan hajoji da ayyukan ba da hidima guda takwas, wadanda suka ba da tasiri kan alkaluman CPI, akwai guda shida daga cikinsu wadanda farashinsu suka karu, yayin da wasu biyu kuma suka ragu.

A watan Yuli kuma, farashin abinci, da taba, da giya, sun ragu da kashi 0.1 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, lamarin da ya haddasa raguwar alkaluman CPI da kashi 0.04 bisa dari. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China