in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF ya sake gyara hasashen da ya yi kan bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin
2017-07-24 13:25:03 cri

A yau Litinin ne, asusun ba da lamuni na duniya wato IMF ya kaddamar da rahoto game da hasashen tattalin arzikin kasa da kasa a birnin Kuala Lumpur, hedkwatar kasar Malaysia, wanda ya sabunta wasu fannoni,kana ya kara has ashen da yake yi game da yawan karuwar tattalin arzikin kasar Sin a bana da kuma shekara mai ya zuwa kashi 6.7 cikin dari da kuma kashi 6.4 cikin dari.

Wannan shi ne karo na 3 da asusun na IMF ya kara hasashen da ya yi kan bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2017 da muke ciki.

Asusun ya yi nuni da cewa, dalilin da ya sa ya gyara hasashen da ya yi kan bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin shi ne domin kasar Sin ta yi fintikau sosai ta fuskar ci gaban tattalin arziki a watan Janairu zuwa Maris na bana, kuma ana sa ran cewa, nan gaba gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da ba da taimakon kudi wajen bunkasa tattalin arziki. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China