Jiya Talata cibiyar nazarin kasuwanci kan Internet ta kasar Sin ta kaddamar da rahoton sa ido kan adadin kasuwar yin ciniki kan Internet a farkon rabin shekarar 2017, inda ta bayyana cewa, a cikin farkon rabin shekarar 2017, jimillar kudin yin ciniki a kan Internet ya kai kudin Sin yuan biliyan 13350, wato dalar Amurka biliyan 2032 a kasar Sin, adadin da ya karu da kashi 27.1 cikin dari bisa makamancin lokaci na shekara bara.
Yanzu yin ciniki kan Internet yana shafar sassa daban daban na zaman rayuwar al'ummar kasar ta Sin, ciki had da yin odar abinci daga waje, samun ilmi kan Internet, harkokin sufuri, sayen tikiti, neman soyayya, yin hayar mota, karbar hidimar aikin gida da dai sauransu.
Rahoton ya shaida cewa, ya zuwa watan Yuni na shekarar 2017, yawan wadanda suke aiki cikin kamfannonin ba da hidimomin kasuwanci kan Internet ya wuce miliyan 3 da dubu 100. Kana kuma yawan wadanda ayyukansu suka shafi kasuwanci kan Internet ya zarce miliyan 23 a nan kasar Sin. (Tasallah Yuan)