in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: ana kokarin raya dangantakar abokantaka dake tsakanin Sin da ASEAN
2017-08-07 10:20:45 cri
A jiya Lahadi ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya halarci taron ministocin harkokin waje na Sin da kasashe membobin kungiyar ASEAN, wanda aka gudanar a birnin Manila dake kasar Philippines.

A gun taron, Wang Yi ya taya mahalarta taron murnar cika shekaru 50 da kafuwar kungiyar ASEAN, kana ya bayyana cewa, a matsayin muhimmiyar kungiya dake yankin kudu maso gabashin nahiyar Asiya, kungiyar ASEAN tana samun ci gaba, da zama muhimmin bangare mai tasiri ga yunkurin raya yankin bisa tsarin bai daya, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kungiyar ASEAN wajen inganta kungiyar, da kiyaye matsayinta mai muhimmanci yayin da ake gudanar da hadin gwiwa a tsakanin bangarori daban daban a yankin, da kuma nuna goyon baya ga kungiyar ASEAN, wadda take kara taka muhimmiyar rawa kan harkokin kasa da kasa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China