in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya yi bayani game da manufofin diplomasiyya a tsakanin Pakistan da Afghanistan
2017-06-26 14:49:21 cri
A jiya Lahadi ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kammala ziyararsa a kasar Pakistan, kana ya gana da 'yan jarida tare da manazarcin harkokin waje na firaministan kasar Pakistan Sartaj Aziz, inda ya yi bayani game da manufofin diplomasiyya a tsakanin Afghanistan da Pakistan.

Wang Yi ya bayanna cewa, tun daga ranar 24 zuwa 25 ga wata, ya kai ziyara a kasar Afghanistan da Pakistan bisa gayyatar da aka yi masa, ban da raya dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen biyu, wani muhimmin aikin da ya yi shi ne, shiga-tsakani wajen sa kaimi ga kyautata dangantakar dake tsakanin Afghanistan da Pakistan, da samun sulhu a tsakaninsu bisa bukatun kasashen biyu.

Wang Yi ya jaddada cewa, Sin ba ta tsoma baki cikin harkokin cikin gida na sauran kasashe, ba kuma ta tilasa ra'ayoyinta ga sauran kasashe, kaza lika ba ta shiga harkar siyasa ta iyakar wata kasa. Sai dai idan abokan tana bukata, za ta iya samar da gudummawa.

Kasashen Pakistan da Afghanistan dukkansu na fatan kasar Sin za ta taka muhimmiyar rawa kan wannan batu, wanda hakan ya shaida cewa, sun yi imani kwarai da kasar Sin. A yayin ziyararsa, Wang Yi ya yi shawarwari tare da shugabannin kasashen biyu, ya kuma saurari ra'ayoyi daga bangarori daban daban, a karshe sun cimma daidaito, tare da bayar da hadaddiyar sanarwa ta Sin da Afghanistan da Pakistan. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China