in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya bayyana matsayin Sin kan batun yankin Gabas ta Tsakiya
2017-06-23 11:14:35 cri
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya bayyana matsayin da kasar Sin ta dauka dangane da batun yankin Gabas ta Tsakiya.

Da yake ganawa da 'yan jarida tare da Ministan harkokin wajen Jordan Ayman Safadi a jiya Alhamis, Wang ya ce, duniya ba za ta sami zaman lafiya ba, har sai yankin Gabas ta Tsakiya ya sami zaman lafiya, yana mai fatan za a tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tun da wuri.

Ya ce matsalolin da wannan yanki ke fama da su sun hada da ta kabilanci da addini, da ta yankin kasa a wuri guda, al'amarin da ya sa matakan soja ba za su iya daidaita su ba, sai dai hanyar siyasa mai dacewa da moriyar kowane bangare.

Ban da haka, Wang ya kara da cewa, Sin tana goyon bayan karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya da shiyya-shiyya kan yaki da ta'addanci, domin bayan yakarsu, wasu kungiyoyin 'yan ta'adda na bazuwa a sauran yankuna dake yankin Gabas ta Tsakiya, har ma da duniya baki daya, ya na mai cewa, kamata ya yi kasashen duniya su hada kansu, wajen tabbatar da yaki da ta'addanci, da bazuwar 'yan ta'adda.

Bugu da kari, Ministan ya ce Sin na fatan nemo sabbin hanyoyin raya tattalin arziki, ya na mai alakanta rashin zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya da karancin ci gaba, inda ya ce dole ne a daidaita matsalar daga wannan fanni.

Ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su kara mai da hankali kan batun neman samun ci gaba a wannan yanki, tare da nuna goyon baya ga kasashen dake yankin wajen lalubo hanyoyin samun bunkasa da suka dace da su.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China