Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi kira ga daukacin sassa masu ruwa da tsaki da rikicin kasashen yankin Gulf ya shafa da su hanzarta hawa teburin tattaunawa, kana su warware bambance-bambancen dake tsakaninsu karkashin yarjejeniyar hadin gwiwar kasashen yankin (GCC).
Wang ya bayyana hakan ne jiya Alhamis yayin ganawarsa da takwaransa na kasar Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani wanda ke ziyara a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Ya ce, kasar Sin ta yaba da rawar da kasar Kuwait take takawa na mai shiga na warware wannan takaddama. Ya kuma yi kira ga kasashen duniya, da su taimaka wajen samar da matakan warware wannan matsala a matakin shiyya.(Ibrahim)