in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya halarci taron ministocin harkokin waje game da hadin gwiwar kasashen gabashin Asiya a fannoni 3
2017-08-08 10:41:55 cri

A jiya ranar 7 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya halarci taron manema labaru, bayan kammalar taron ministocin harkokin waje game da hadin gwiwar kasashen gabashin Asiya.

A gun taron manema labarun, Wang Yi ya bayyana cewa, a ganin kasar Sin, nasarori mafiya kyau da aka samu a gun taron su ne, a karkashin kokarin Sin da kasashen kungiyar ASEAN, an kiyaye zaman lafiya a yankin teku na kudancin Sin, ana kuma hadin gwiwa da juna, da mai da bangarori daban daban da batun ya shafa teburin shawarwari.

Wang Yi ya ce, bambanci mafi girma da aka gani shi ne, yayin da kasashen dake kewayen teku na kudancin kasar Sin, da kuma kasar ta Sin suka tabbatar da kyakkyawar makomar yankin teku na kudancin Sin, wasu kasashen dake nesa da yankin sun kyale ci gaban da aka samu, da amincewarsu da nasarorin da Sin da kungiyar ASEAN suka samu, sun kuma bayar da labarai marasa kyau ga kasashen waje.

Haka zalika kuma, batu mafi jawo hankali a gun taron shi ne batun nukiliya a zirin Koriya. Ya ce kasashen duniya sun fara fahimta da nuna goyon baya ga kiran "Koriya ta Arewa, da ta dakatar da aikin harbar makamai masu linzami da na nukiliya, da kuma bukatar Amurka da Koriya ta Kudu su dakatar da yin atisayen soja", kana sun kara dora muhimmanci ga shirin warware batun nukiliya a zirin Koriya cikin lumana, wanda Sin da Rasha suka tsara tare. (Zainab Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China