Ya ce, ya kamata a warware matsalar nukiliyar zirin Koriya cikin zaman lafiya, sabo da yaduwar makaman nukiliya tana kalubalantar zaman lafiyar duniya kwarai da gaske. Haka kuma, ya yi kira ga kasashen duniya da su dukufa wajen cimma burin kawar da makaman nukiliya a fadin duniya, musamman ma kasashen da suka riga suka samun makaman nukiliya.
Cikin jawabinsa, Mr. Guterres ya mai da yaduwar makaman nukiliya, ta'addanci, sauyin yanayi da kuma rashin daidaiton zaman al'umma da dai sauran matsaloli a matsayin manyan kalubalolin dake gaban kasa da kasa a halin yanzu, inda ya bukaci a hada kai domin fuskantar wadannan matsalolin. (Maryam)